- Karanta dukan bayanin kariya na kasa kafin amfani da na'urarka.
- Amfani da wayoyin caja, da adafta marasa asali, ko kuma batir na iya haifar da gobara, fashewa ko ya janyo wasu hadari daban.
- Yi amfani da kayayyanki na asali kadai da su ka dace da na'urarka.
- Yi amfani da wannan na'urar a jeri na yanayi tsakanin 0 ° C ~ 40 ° C, kuma adana wannan na'ura da kayan sa a jeri na yanayi tsakanin -20 ° C ~ 45 ° C. Amfani da wannan na'urar a wurin da karfin zafin ya wuce iyakar sa na iya lalata na'urar.
- Idan na'urarka tare da batir aka gina, kada kayi ƙoƙarin canza batir din kai da kanka don kauce wa lalata batir din ko na'urar.
- Yi cajin wannan na'urar kawai tare da waya da adfta sa na asali. Amfani da wata adafta daban na iya haifad da gobara, bugu na wutar lantarki, ya lalata na'urar da kuma adftan.
- Idan cajin ya kammala, cire adaftan daga na'urar kuma daga wutar lantarki. Kar a caja na'urar fiye da awowi 12.
- Kada kayi ƙoƙarin gyara fulog ko igiyar wutar da kanka, kuma don Allah a cire haɗin da wutar lantarki kafin gogewar caja.
- Kada a saka na'urar ko tsofaffin batir a cikin sharar gida. Idan ba a kula dashi sosai ba, batir zai iya fashewa ko kuma ya kama wuta. Bi umarninka na gida lokacin jefad da na'urar, batura, da wasu kayan haɗi.
- Batir dole ne a sake juyawa ko a saka shi daban daga sharar gida. Rashin kulawa da batir sosai na iya haifar da gobara ko fashewa. Yi watsi ko saka na'urar a kwadon shara, batir da kayan haɗi
bisa ga dokokin gida.
- Kar a kwance, a doka, a murkushe, ko ƙona batir. Idan akwai alamar lalacewa, dakatar da amfani da baturin nan da nan.
- Kada ka rage karfin wutan batiri don kauce wa zafi, konewa, ko wata ɓarna.
- Kada a sanya batir a wuraren da ake tsananin zafi. Zafi na wuce iyaka na iya jawo da fashewa.
- Kada a kwance, a doka, ko murkushe batir don kauce wa rushewar batir, zafi na wuce iyaka, ko fashewa.
- Kada ka ƙona batir don kauce wa gobara ko fashewa.
- Idan akwai alamar lalacewa, dakatar da amfani da baturin nan da nan.
- Tsaya da amfani da batir idan yana nuna alamun canza kala, gurɓatawa, yawan zafi na wuce iyaka, ko ƙumburi
- Bar na'urarka bushe. Kada ka ajiye ko amfani da na'urar da kayan haɗi a cikin yanayi mai zafi da mai zafi ko kusa da wuta a bude.
- Don hana yunkurin garanti, kada ka kwance ko gyara na'urar da kayan haɗin sa. Idan wani ɓangare na na'urar ba ya aiki yadda ya kamata, tuntuɓi goyon bayan abokin ciniki na Mi ko kai na'urarka zuwa wurin gyarawa na asali.
- Don hana yiwuwar lalacewa na ji na kunni, kada ku saurara da kara mai yawa ma tsawon lokaci.
- Kafin gogewa da aikin gyare-gyare na na'urar, rufe dukkan manhaja kuma cire haɗin na'urar daga dukkan wasu na'urori/ igiyoyi.
- Ayi amfani tufafi wanda ya bushe, mai laushi mai tsabta don shafe na'urar da kayan haɗi. Kada kayi amfani da kayan kemikal ko sabulu ka wanke na'urar ko kayan haɗi.
- Kada ayi amfani da kayan dake fitar zafi kamar microwave ko na'urar bushewar gashi don busar da na'urar da kayan haɗin sa.
Kariya na yaro
- Bar na'urar da dukan kayan haɗi nesa da yara. Kada ka bari yara suyi wasa dashi, su sa a baki, ko su haɗiye na'urar ko duk wani kayan haɗinsa don kauce wa haɗarin numfash ko maƙura.
Yin kira na hanzari
- Saboda bambancin hanyar sadarwa na sabis da sauran bambance-bambance na yanki, na'urar bazai iya yin kira a duk yankuna da kuma dukan yanayi ba. Kar ka dogara kawai akan na'urar ka yi kira mai mahimmanci ko kira na hanzari. Ba'a iya kiran waya da Mi Pad.
Matakai na kariya
- Duba dukan wasu dokoki da ke takaita amfani da wayoyi a cikin kebabbun al'amuran ƙira da wasu wurare.
- Kada kayi amfani da wayarka a wasu wuraren dake iya fashewa, da wuraren da ake amfani da man fetur, ƙarƙashin ƙasa a kan jiragen ruwa, man fetur ko canja wuri kayan kemikal ko wurare na ajiyan kaya, wuraren da iska ke dauke da kemikal ko barbashi, kamar su hatsi, ƙura, ko garin karfe. Yi biyayya da duk alamomin da aka baza don kashe waya mara waya kamar na'urarka ko kayan aiki na rediyo. Kashe wayarka ta hannu ko na'ura mara waya a lokacin da kake cikin wani wuri mai fashewa ko wuraren da aka nuna kashe "hanyoyin rediyo biyu" ko "na'urorin lantarki" don kaucewa haduwa tare da aikin fashewa.
- Kada kayi amfani da wayarka a ɗakuna na asibiti, ɗakunan gaggawa na asibiti, ko ɗakunan kulawa mai tsanani. Bi wadannan dokoki da ka'idoji na asibitoci da wurare na kiwon lafiya. Don Allah tuntuɓi likitan ku da kamfanin waya don tantancewa idan aiki da na'urarku zai iya shafan aikin na'ura na likita. Don kaucewa shisshigi tare da na'urar bugun zuciya, bar sarari akalla na 15 cm tsakanin wayar hannu da na'urar bugun zuciya. Don cimma wannan, yi amfani da waya a kan kunnenka na biyu zuwa na'urarka na auna bugun zuciya kuma kada ka sa shi a aljihun ƙirji. Kar ka yi amfani da wayarka kusa da na'urar ji ta kunni, na'urar cochlear da aka sanya a cikin kunni, da sauransu. don ka kauce samun cikas tare da kayan aikin liita.
- Yi biyayya Ga dokokin kariya na jiragen sama da kuma kashe na'urarka a cikin jirgin lokacin da ake bukata.
- Idan kana tuƙin mota, yi amfani da na'urarka daidai bisa ga dokoki da tsari na hanyoyi da suka dace.
- Don kauce wa bugu na walƙiya, kada kayi amfani da na'urarka a waje a lokacin hadari mai iska.
- Kada kayi amfani da na'urarka ka yi kiran waya yayin da yike caji. Ba'a iya kiran waya da Mi Pad.
- Kada kayi amfani da na'urorinka a wuraren da ake zafi sosai kamar dakunan wanka. Yin hakan zai iya janyo bugu na wutar lantarki, jin ciwo, gobara, da lalacewar caja.
- Duba dukan wasu dokoki da ke ƙuntata amfani da na'urorin mobayil a cikin kebabbun al'amuran ƙira da wasu wurare.
- Lokacin amfani da filashi, kada ka kawo ftilan kusa da idanu mutane ko dabbobi don kiyaye lafiyan idanu.
- Idan na'urar yayi zafi kwarai, kada ka bari ya hadu da fatan jikinka ma wani tsawon lokaci don kauce wa ƙonin jiki.
- Idan allon ya fashe, don Allah ka yi hankali ga gefensa dake da kaifi ko gutsutssi wanda zai sa a ji ciwo. Idan na'urar ya faffashe ko ya watse bayan karo da wani abu mai karfi ko wani bugu mai karfi, kada ka taɓa ko ƙoƙarin cire sashin dasu ka fashe. Tsayar da amfani da wannan na'urar sai ka tuntuɓi sabisin Bayan-Sayarwa na Xiaomi nan da nan.
Sanarwa na tsaro
- Sabunta sarrafa tsarin na'urarka ta hanyar amfani da siffa na sabuntawar manhajar da aka gina dashi, ko ziyarci kantuna na sabis ɗinmu na asali. Sabunta manhaja ta wasu hanyoyi marasa asali zai iya lalata na'urar ko janyo asarar bayanai, matsaloli na tsaro, da wasu haɗarin daban.
Yanayin karatu
- Akwai wannan siffar ne kawai a cikin na'urorin Mi dasu ka dace.
- Yanayin karatun yana rage girman haske fitilan allo da kansa don kyautata kallon allon da idanunku.
- Yana canzawa zuwa yanayin karatu:
Akwai hanyoyi biyu na kunnawa da kashewar Yanayin Karatu:
1. Ja zuwa kasa daga saman Allon farko don nuna inuwar Sanarwa, sa\'an nan kuma danna maɓallin Yanayin karatu.
2. Jeka cikin Saittuna > Nunawa > Yanayin Karatu. A kan wannan allon, zaka iya tsarawa don kunnawa ko kashewar Yanayin karantawa da kansa kuma ka daidaita yanayin zafi na launi.
1. Doka na 20-20-20: An bada shawarar yin kallon wani abu da ke da nisan takawa 20 ma sakan 20 a kowane minti 20.
2. Kiftawa: Don taimakawa bushewa idanu, yi kokarin rufe idanu ma sakan 2, sa'annan ka bude su sai ka kifta da hanzari ma sakan 5.
3. Mai da hankali: Aiki ne mai kyau ma idanunka don kallon allonku daga wuri mafi nisa da za ku iya gani, ya bi ma mayar da hankali a kan yatsa ku sa minti cm 30 a gaban idanun ku na dan lokaci kadan.
4. Naɗawar ido: Naɗa idanunku a kowane lokaci, sai ka huta da kuma naɗa su ta wata hayan daban.
5. Tafin hannu: Goga tafin hannunka tare don samar da dumi kafin a danna su a hankali da idonku ma 'yan sakan.